Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Sojojin Yemen sun tabbatar da jerin wuraren da za su kai hari a kai idan Saudiyya ta aiwatar da barazanarta na kai hari ga kamfanin man fetur a babban birnin Sana'a.
Sojojin Yemen a cikin wata sanarwa sun yi kira ga dukkan 'yan ƙasar Saudiyya da su fice nan take kuma su nisanta daga wuraren da za su kai hari a kai idan har Saudiyya ta kai hari ga abin da ta sanar a babban birnin Sana'a.
Sojojin Yemen sun bayyana cewa wuraren da zasu hara sune: "Hedkwatar kamfanin Aramco a Dammam. Filin jirgin sama na Khalid a Riyadh. Matatar Riyadh ta kamfanin Aramco."
A baya, sojojin Yemen sun gargadi Saudiyya cewa duk wani hari a babban birnin Sana'a zai fuskanci mayar da martani mai tsanani da raɗaɗi a babban birnin Saudiyya, Riyadh. Kuma lokacin da Saudiyya ta tabbatar da wuraren da zata kai hari a babban birnin Sana'a, sojojin Yemen sun gargadi dukkan ma'aikata da 'yan ƙasa da ke kusa da duk wata cibiya ta kamfanin man fetur na Aramco da su fice kuma su nisanta, domin halastattun wurare ne na ga sojojinmu. Sun kuma sake maimaita gargadin ga dukkan ma'aikata daga ƙwararru, injiniyoyi, da ma'aikata a dukkan cibiyoyin man fetur na Saudiyya da nisantar kasancewa a wuraren da suka zama hadafin sojojinmu don kada su jefa rayukansu cikin haɗari, ko waɗanda aka kai hari a baya ko wasu. Sun kuma sake maimaita gargadin ga kamfanonin jigilar jiragen sama a fagage da filayen jiragen sama da matafiya da ma'aikatan da ke cikinsu waɗanda aka sanar a baya.
………………….
Ra'ayinka